Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : an soke mukamin babban Mufti na kasar wanda ke wakiltar babbar hukumar addinin Musulunci a kasar ta hanyar umarnin shugaba Bashar al-Assad.
Dokar, ta ce an aike da Sheikh Ahmad Badreddine Hassoun mai shekaru 72, zuwa ritaya, Inda aikinsa zai koma hannun majalisar shari'ar musulunci, hukumar dake karkashin ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar.
Daga yanzu majalisarsa ce za ta rika tantance kalanda kuma ta kuma ba da ra'ayi kan harkokin addini, a kokarin da gwamnati ke yi na fadada sa ido kan al’amura na addini.
342/